Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kashe Mutane Akalla 30 A Maiduguri


Sojoji suna tsaye a gaban shagunan da aka kona a Maiduguri
Shedun gani da ido a birnin Maiduguri, arewa maso gabashin Nigeria sun zargi sojoji da laifin bude wuta akan farar hula, harma suka kashe akalla mutane talatin.

Yan jarida da ma’aikatan asibiti sun baiyana cewa yawancin wadanda aka kashe, da alama farar hula ne. Sunce sojojin sun bamkawa gidaje da kantuna wuta.

Mazauna birnin sunce jiya litinin wannan tarzoma ta auku bayan wani bam ya tashi akan sojojin da suke sintiri ya raunana sojoji guda biyu.

Jami’an soja basu tabbatar ko musunta rahotanin cewa sojoji sun bude wuta akan farar hula ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG