Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Yi Arangama Da ‘Yan Boko Haram A Damboa


Sojan Najeriya.

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kasha mayakan Boko Haram su 38 a lokacin da ta tarwatsa wani shirin da suka yin a kai farmaki a garin Damboa a Jihar Borno.

Rundunar sojojin Najeriya ta fada yau alhamis cewa ta kashe mayakan Boko Haram su 38 a wasu hare-haren da ta kai kan su a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya a Maiduguri, Kanar Muhammad Dole, ya ce wasu sojoji dake aikin sintiri sun wargaza wani yunkurin da mayakan Boko Haram suka yin a kai farmaki kan garin Damboa da wani barikin soja dake can da asubahin yau, suka yi barna mai yawa ma tsageran.

A cikin wata sanarwar da ya aikewa da ‘yan jarida ta hanyar Imel, Kanar Dole ya ce, “an kasha ‘yan ta’addar Boko Haram su 38 a wannan fadan, wasu kuma sun gudu da raunuka dabam-dabam a jikinsu.” Ya kara da cewa an lalata motocinsu guda uku.

Kanar Dole yace an gano nakiyoyi da bama-bamai a cikin mota guda. Haka kuma an samu muggan makamai, ciki har da manyan bindigogi na mashin-gan.

An kasha soja guda daya, yayin da wasu guda biyu suka ji rauni a wannan artabu da aka yi.

Sanarwar ta Kanar Dole, ta kara da cewa, “Sojojin kasa da jiragen saman yaki sun a farautar ‘yan ta’addar da suka gudu a nan yankin Damboa da kauyukan da suke kewaye da nan.”

Garin Damboa dai yana da tazarar kusan kilomita 90 a kudu maso yamma da Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A watan Mayun shekarar da ta shige ne shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kafa dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa domin murkushe kungiyar Boko Haram da kuma kawo karshen tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG