Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Na Kara kaimi Domin Kakkabe 'Yan Taadda A Afghanistan


AFGHANISTAN -- Afghan Army soldiers in Kandahar, February 28, 2018

Sojojin Amurka na kara kaimi domin ganin an kakkabe kungiyoyin IS dana taliban dake kasar ta Afghanistan

Sojojin Amurka na kara kaimi wajen yakin da akeyi a Afghanistan na kokarin ganin a fatattaki kungiyar ‘Yan taaddan IS dake arewacin dama kungiyar Taliban da suke Kudanci dama yammacin kasar.

Wannan karin matsin kaimin ya biyo bayan Karin kokarin da Afghanistan din keyi ne na ganin ta kakkabe gabadayan kungiyar IS, kana ta kokarta wajen shawo kan kungiyar Taliban da ta kawo karshen banbancin dake tsakanin ta da gwamnati tazo ayi sulhu.

Mahukunta suka ce ga bisa dukkan alamu wannan yunkuri na samun nasara musammam ma a arewacin kasar, inda harin ranar Jumaa yayi dalilin mutuwar mutane da dama a arewacin ciki ko harda babban kwamandar kungiyar ta IS Wacce wata bangare ce ta kungiyar dake Afghanistan din.

A jiya asabar dai Sojojin na Afghanista sun tabbatar da mutuwar kwamandar na IS wato Qari Hekmutullah, sakamakon harin da aka kai a gundumar Darzab inda yake nan ne daya daga cikin tungan yan kungiyar ta IS.

Gwamnan lardin Maulvi Latifullah ya fada wa wannan gidan radiyon cewa ko baya ga kashe Hekmatullah shima na hannun damar sa an kashe shi, domin ko an birne dukkan su biyu a tsakad dare a kusa da wani kauye, inda kalilan daga cikin ‘yan kungiyar ne suka halarci janaizar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG