Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Da Ke Libya Sun Yi Nasara Akan 'Yan Ta'adda


Sojojin Amurka da Nijar sun kulla yarjejeniya
Sojojin Amurka da Nijar sun kulla yarjejeniya

Sojojin Amurka sun samu nasarar kashe wasu 'yan taadda akasar Libya sakamakon harin da suka kai a kudu maso yammacin kasar.

Sojojin Amurka sunce sun samu nasarar kashe wasu ‘yan taadda biyu a wani harin da suka kai ta sama a kudu maso yammacin Libya a jiya asabar, aci gaba da kokarin da rundunar keyi na ganin ta hana ‘Yan taadda samun matattara a kasar ta Libya.

Harin wanda yakai har wajen birnin Ubari an shirya ne tare da aiwatar dashi da hadin kan gwamnatin kasar dake birnin Tripoli wadda ita ce gwamnatin da kasashen duniya suka yarda da halarcin ta, wannan sanarwan dai na kunshe ne a cikin bayanan da Kwamanda Amurka mai kula da kasashen Africa ya fitar.

Sanarwan ta kara da cewa, bincike ya tabbatar da cewa sakamakon wannan harin ba wani farin hula da ta rutsa dashi.

Wani wanda yake a Ubari, ganau ne ya shaidawa kanfanin dillacin labarai na Reuters ta wayan tarho cewa sunji karar fashewar wani abu ne da tsakar rana.

Wani gida dake wurin da ake kira Fursan inda wannan bomb din ya sauka yayi dalilin mutuwar mutane biyu, wani dan taliki dake makwabtaka da wannan gidan yace gidan da wannan bomb ya auka mawa gida ne da ake yawan ganin baki na yawan shigar sa.

Wasu kafafen yada labarai na kasar ta Libya sun ta nuna hotunan gawar wani yayi kaca-kaca, domin harma kai ya fita daga gangan jiki, kana anga mota tarwatse.

Sojojin na Amurka dai suna kai hari jefi-jefi tun a yan shekarun da suka gabata, da niyyar auna ‘yan taadda.

Ko a shekarar data gabata sai dai Amurka tace ta samu nasarar kashe ‘yan taadda da dama a kudanci kasar ta Libya da niyyar hana su taruwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG