Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Kashe Wani Shugaban Al-Qaida A Libya


Wani shugaban al-Qaida

Sojojin Amurka dake nahiyar Afirka sun kashe wani shugaban al-Qaida Musa Abu Dawud lamarin da ita kungiyar dake Magreb ta tabbatar

Daya daga cikin manya-manyan shugabannin kungiyar Al-Qaida na cikin ‘yan taadda biyu da aka kashe a wani harin hadin gwiwa tsakanin sojojin Amurka da na Libya a ranar Asabar, wanda ya faru kudu maso yammacin kasar Libya.

Bada jumawan ba, sojojin na Amurka sun tabbatar da kai wannan harin a kusa da garin Ubari, amma sunce ‘yan ta’adda biyu kawai aka kashe.

Rundunar mayakan Amurka mai kula da shiyyar Africa, ta tabbatar a jiya laraba cewa ba shakka ankai harin, wanda shine irinsa na farko da aka auna kungiyar Al-Qaida a kasar Libya, inda aka kashe Musa Abu Dawud, wanda shine yake horas da bangaren ‘yan kungiyar ta Al-Qida dake yankin arewacin Afirka da ake kira Magreb.

Kwamandan na Amurka dake Africa ya ce Dawud din shine yake samar da makamai da kudi ga kungiyar dake yankin na Magreb, wanda hakan ya sa kungiyar kewa Amurka barazana da wasu muradun yammacin duniya a yankin.

A jiya dai wata kungiya mai alaka da -Qida ta tabbatar da mutuwar Dawud a harin da sojojin na Amurka suka kai kamar yadda kafar tattara bayanan sirri da ake kira SITE a takaice wacce take maida hankali kan barazanar da kungiyoyin 'yan ta'adda suke yi.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG