Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Cadi Sun Kashe Wani Kwamandan Al-Qaida A Mali.


Wani hoto da aka nuna cikin watan Dismeba na Abdelhamid Abou Zeid, daya daga cikin shugabannin al-Qaida a yankin Mgareb.
Shugaban kasar Cadi Idris Deby yace dakarun kasarsa da suke Mali sun kashe wani kwamandan al-Qaida Abdelhamid Abu Zeid lokacin wani gumurzun a arewacin Mali.

Babu cikakken bayani a daren jiya jumma’a, duk da haka shugaba Deby ayce dakarunsa sun kashe shugabannin masu ikirarimn Jihadi biyu ciki harda Abu Zeid.

Rahotanni a kafofin yada labadan Aljeriya da faransa sun ce an dauki samfur daga dangin kwamandan da ake kashen, kuma hukumomi suna kokarin awo domin tanatance gawarda aka samu a aarewacin Mali.

Sojojin Cadi suna tallafawa a wani yunkuri da Faransa take yiwa jagoranci wajen ganin an tusa keyar masu ikirarin Islama a Mali.

A jiya Jumma’a shugaba Deby ya jagoranci jana’izar sojojin kasar 26 da aka kashe.
XS
SM
MD
LG