Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Dake Filin Jirgin Saman Maiduguri Sun Yi Bore


Manyan sojojin dake Borno
Manyan sojojin dake Borno

Yunkurin sakewa sojojin dake filin jirgin saman Maiduguri zuwa Marti ya harzuka su suka tada bore saboda a cewarsu sun yi shekara uku a Maiduguri, maimakon a turasu wani sabon wuri kamata ya yi a mayar dasu inda aka kawo su

Jiya da maraice a misalin karfe shida na yamma aka fara jin karan harbe-harben bindiga a filin jirgin saman birnin Maiduguri.

Daga bisani aka gane cewa jami'an sojojin dake filin ne suke harbin, suna boren nuna rashin amincewa da kokarin da manyansu su keyi na neman sauya masu wurin aiki zuwa garin Marti.

Harbe harben ya firgita mazauna anguwar da tashar jirigin saman yake, musamman maniyatta aikin hajji da yanzu suke cikin filin inda ake tantance su gabanin tashinsu.

Duk da tsawon lokacin da sojojin suka kwashe suna harbe harben babu wani rahoton salwantar ran wani mutum ba.

Sojojin da suka rika harbe harben na korafin cewa sun kwashe kimanin shekaru uku a filin daga. Maimakon a mayar dasu inda suka fito bayan shekara daya, yanzu ana yunkurin sauya masu wurin aiki. Idan hakan ya faru za'a dauka tamkar yanzu aka kawosu daga barikinsu. Wanna halin ya haifar da turjiyar da sojojin suka yi.

Ta bakin wani daga cikin sojojin, "yanzu shekarun mu uku a Maidugurin nan, tun watan Fabrairun 2016 aka turomu nan. Sai da yamman nan wani Manjo da wani Kanar suka shigo wai mu tattara kayanmu zamu koma Marti. Bayan shekara uku kuma sai a turamu Marti mu sake wani sabon zama? Da zarar mun kai Marti zasu fara mana sabon kidayan wa'adi ne".

To sai dai babu wani bayani daga bangaren manyan jami'an sojojin, musamman na 'Operation Lafiya Dole' dangane da wannan boren da sojojin suka yi.

A saurari rahoton Haruna Dauda Biu

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG