Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gamayya Sun Kashe Mutane 68 a kasar Yemen


Ana cigaba da barin wuta a Yemen
Ana cigaba da barin wuta a Yemen

Kamar yadda aka yi fargabar zai faru, tun bayan kisan tsohon Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh rikicin Yemen, wanda tun dama ya tafasa, ya kazance ta yadda aka shiga luguden wuta da kai hare-hare kusan kulluyaumin. Fadan da ake ganin ana yi ne tsakanin Saudiyya da Iran a fakaice.

Mutane wajen 68 sun mutu sanadiyyar hare-haren jiragen sama da sojojin gamayya karkashin jagorancin Saudiyya su ka kai a Yemen a rana guda kawai, a cewar wani babban jami’in MDD da ke kasar a jiya Alhamis.

Fararen hula 54, ciki har da yara 8, sun halaka bayan da wani jirgin sama yay a kai hari kan wata cinkusasshiyar kasuwa a lardin Taez ranar Talata. Mutane 14 kuma sun mutu ne a wani samamen da aka kai lardin Hodeida da ke yankin Red Sea duk a rana guda, a cewar bayanin na babban jami’in gudanarwa na MDD Jamie McGoldrick.

Hare-haren biyu sun sa adadin fararen hulan da aka kashe a Yemen a hare-haren sojojin gamayyar da Saudiyya ke jagoranta sun kai sama da 100 a cikin kwanaki 10 kawai da su ka gabata.

‘Yan tawayen Houthi sun kama Sana’a babban birnin kasar Yemen a karshen shekarar 2014. Gamayyar sojojin da Saudiyya ke jagoranta kuma ta mai da martani a watan Maris na 2015 ta wajen kaddamar da yaki kan ‘yan tawayen. Tun sannan, a cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), hukumomin lafiya sun bayar da rahotannin mace-macen mutane dama da 8, 700 sanadiyyar tashe-tashen hankula baya ga mutane 50,000 da su ka jijji raunuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG