Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Iran 19 Sun Mutu Bisa Kuskure


Kimanin sojojin Iran 19 ne suka mutu, wasu 15 kuma suka jikkata bisa kuskure, a wani hatsarin da ya faru a lokacin atisayen harbi na soja.

Gidan talabijin na Iran ya ruwaito cewa “lamarin ya faru ne a yankin kudancin kasar a kan iyakar Bandar-e dake gefen tekun Gulf na Oman, a lokacin wani atisayen sojin rowan a jiya Lahadi.”

Wani jirgin rakiya Jamaran ya harba makaman da suka fada kan bututun Mai na Konarak.

Kafar talabijin din ta kara da cewar “Makaman sun kai ga bututun ne bayan da aka sauya inda aka auna su, ba tare da ba da tazara tsakanin sabon bagiren da bututun Man yake ba.”

Da ma dai sojojin ruwan Iran su kan yi irin wannan atisayen lokaci-lokaci a yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG