Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Iraqi Na Kara Dannawa Yammacin Mosul


Dakarun Iraqi da Amurka ke marawa baya na kara kutsawa cikin Yammacin Mosul a yau lahadi domin jan daga a wajen da dakarun Da’esh ke rike dashi.

Daga nesa ana hangen hayaki a yau lahadi daga sararin samaniyar birnin a yayin da ake jin karar fashewar nakiyoyi.

Tun daga lokacin da gwamnati ta fara kutsawa cikin yammacin birnin a farkon 19 ga watan Fabrairu, Kwamandojin Amurka da na Iraqi sun bayyana irin tsananin jajircewar da dakarun 'yan tsagerun sukayi wajen jan tunga a biranen da suke da matukar amfani a kasar da yaki ya tarwatsa.

Dakarun gamayyar da Amurka ke jagoranta , wadanda aka kai musamman domin horaswa da kuma bada shawarwari, sun taimaka wa dakarun Iraqi wajen yakin na Mosul.

Dakarun na Iraqi sun sake kwace bangaren gabashin birnin a wannan shekarar bayan kazamin harin da suka kai a watan Oktobar bara.

Major Janar Maan Al-Saadi na dakarun Iraqi ya fadawa kafar yada labarai ta Faransa cewa “Kusan kaso uku “ na yammacin Mosul na karkashin Ikon Dakarun Iraqi ne.

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG