Sojojin Mali sun hallaka ‘yan bindiga wajen 30 a wani samamen da su ka kai, a cewar rundunar sojin kasar jiya Jumma’a, wanda shi ne na baya bayan nan a tashin hankalin da ake yi a wannan kasa ta Yammacin Afurka da yaki ya daidaita.
Sojojin na Mali sun bayyana kashe abin da su ka kira, “’yan ta’addan” ne ta kafar tiwtter kuma su ka ce al’amarin ya faru ne daura da iyakar kasar da Burkina Faso Mai Makwabtaka da ita, da yammacin ranar Alhamis.
Ta kara da cewa ta kuma kwato wasu mashuna guda 25 da wasu kayan aiki, ba tare da wani cikakken bayani kan wannan harin ba.
Firaministan Mali Bounbou Cisse na karfafa sojojin kasar garin Kidal.
Kasar ta Mali na kokarin shawo kan wani tawayen da ya barke a 2012 da suna Islama, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar dubban sojoji da fararen hula tun sannan.
Duk da kasancewar dubban sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya, wannan tashin hankalin ya game yankin tsakiyar kasar sannan ya yadu zuwa kasashe makwabta irin su Burkina Faso da Nijar.
Facebook Forum