Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kama ‘Yan Boko Haram Masu Yawa


Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno
Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno

Rundunar sojan ‘kasa ta Najeriya ta fitar da sanarwar cewa ta samun nasarar fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram daga dajin Sambisa, tare da kame wasu manyan kungiyar guda biyu.

A cikin sanarwar kanal Sani Usman Kuka Sheka, yace ‘yan ta’addar da suka yi kokarin tserewa daga dajin Sambisa sakamakon ruwan wuta da rundunar sojan sama tayi musu. Hakan ya basu damar kame wasu da hallaka wasu da dama, kuma suka gano makamai masu yawa.

Sanarwar tace an kuma kwace wasu motoci guda bakwai da kuma babura da harsashe da alburusai wadanda maharan ke amfani da su, haka kuma har yanzu suna kokarin farauto wadanda suka gudu.

Mataimakin Kanal Sani Usman Kuka Sheka, yayiwa wakilin Muryar Amurka karin haske game da wannan nasara da rundunar ta ce ta samu.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

XS
SM
MD
LG