Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Saman Najeriya Sun Yi Kwanaki Goma Suna Lugudan Wuta kan 'Yan Boko Haram


Air Marshall Abubakar Sadique, hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya
Air Marshall Abubakar Sadique, hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya

A cikin kwanaki goma da mayakan saman Najeriya suka yi suna lugudan wuta kan sansanin 'yan Boko Haram a dajin Sambisa kwamandoji 'yan ta'addan da dama suka halaka.

Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Abubakar Sadique ya ce dakarunsa sun hango yadda wasu daga cikin jagororin mayakan kungiyar Boko Haram ke kokarin sake tattaruwa a cikin dajin Sambisa.

Ba tare da bata lokaci ba, inji hafsan hafsoshin, dakarunsa suka afka masu inda suka kashe da dama cikinsu.Yana mai cewa sunan wannan farmakin shi ne lugudan ruwan wuta saboda sun fahimci cewa akwai wani kokari da 'yan ta'addan ke yi su sake kafa wani sansani cikin dajin Sambisa.

Makasudin farmakin shi ne dakile duk wani matakin da 'yan ta'addan suka dauka bai tabbata ba. Dalili ke nan da sojojin saman suka kwashe kwanaki goma suna lugudan wuta kan 'yan ta'addan. Ta bakin Air Marshall Sadique sun samu biyan bukata da gaske. Lokacin da suka kare kai lugudan wutar babu alamar 'yan ta'addan a wurin.

Duk da nasarorin da suka samu har yanzu suna cigaba da shawagi a sararin samaniya, inji Air Marshall Sadique.

Muhammad Inusa Barnawa masanin harkokin yakin sama a Najeriya yana mai cewa koda an tura sojojin kasa idan babu na sama babu abun da zasu iya yi. Dole ne sojojin sama su fara hari daga sama kafin na kasa su shiga. Muddin aka karya lagwonsu daga sama a kasa kuma ba zasu sami wani karfi ba.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG