Hukumomin Siriya sun bayyana a wata rubutacciyar takarda cewa, sojojin gwamnati sun samu dannawa zuwa cikin wasu muhimman yankuna da ke arewa maso gabashin birnin Manbij da ke karkashin Aleppo.
Sojojin na Siriya sun ce su na masu bayar da tabbacin shirin kare dukkannin 'yan Syria da ma daukacin mazauna cikin birnin.
Kungiyar Dakarun kurdawa Masu Kare Siriya (YPG, a takaice) wadda ita ce babbar kungiyar mayakan Kurdawa a Siriya, ta yi kira ga gwamnatin Bashar al-Assad a yau din nan Jumma'a da ta mayar da Manbij a karkashin kulawarta don ta kare yankin daga barazanar hare-hare daga kasar Turkiyya.
"Mu na masu gayyatar gwamnatin Siriya, wadda mu ma wani bangare ne na ta, da ta tura sojojinta don su kwace wadannan wuraren don su kare Manbij daga duk wata barazana daga Turkiyya," a cewar kungiyar ta YPG a takardar bayanin.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 18, 2021
Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Na Bukatar Sabon Salon Gudanarwa-Dr. Ngozi
-
Fabrairu 18, 2021
Guterres Ya Yi Kiran a Samar Da Tsarin Bai Daya Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 16, 2021
Kungiyar WTO Ta Gabatar Da Sabuwar Shugaba Ngozi Okonjo-Iweala
-
Fabrairu 16, 2021
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Aminta Da Riga Kafin AstraZeneca