Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Sudan Ta Kudu Tamkar Sojojin Kabilar Dinka Ne - Janar Cirillo


'Yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu a Uganda suna jiran a tantancesu

Wani babban hafsan soji a Sudan ta Kudu Janar Thomas Cirillo, yayi murabus, yana zargin shugaba Salva Kiir, cewa ya maida rundunar mayakan kasar tamkar ta kabilanci ce mai biyayya ga kabilarsa ta Dinka.

Janar Thomas yace rundunar sojojin kasar da ake kira Sudan People's Libration Army ko SPLA a takaice, yanzu tana aiki ne karkashin majalisar dattijan kabilar Dinka, mai makon tayi aiki damuradun kasar.

Amma kakakin fadar shugaban kasar Sudan ta Kudun Ateny Wek, wanda yayi magana cikin shirin talabijin na Muryar Amurka da ake kira South Sudan in Foucs ranar Litinin, ya karyata wannan zargi da Janar Thomas yayi.

Ahalinda ake ciki kuma, jami'ai a Somalia da kuma yankin Somaliland da ya balle, suna zargin jami'an kasarta Somaliland da karban cin hanci domin su amince a kulla yarjejeniya da hadaddiyar daular Larabawa ko UAE, domin ta kafa sansanin sojoji a birnin Berbera mai tashar jiragen ruwa, kamar yadda babban Oditan kasar yace.

Odita Janar Nur Jimale Farah yana cikin masu nazari wadanda suke tambayar cancantar kulla wannan yarjejeniya, wacce da gagarumar rinjaye majalisar dokokin yankin Somaliland ta amince da kudurin ranar Lahadi da ta shige.

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG