Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soke Zaben Dan Majalisar Tarayya A Gombe Ya Jefa APC Cikin Wani Sabon Rikici


Alamar APC

Rigimar jam'iyyar APC a jahar Gombe na kara sukurkucewa sakamakon irin hukuncin da kotu ta yanke bayan soke zaben Dan Majalisar Wakilai da kuma irin fassarar da ake ma hukuncin

Baya ga soke zaben kujerar Dan Majalisar Tarayya da APC ke kai a Gombe, jam’iyyar ta sake gamuwa da wata matsala ta hana ta shiga zaben da za a sakena kujerar Dan Majalisar Wakilan na Karamar Hukumar Akko ranar 19 ga watan Disamban wannan shekarar.

Sakataren Mulki a Hukumar Zaben Jahar Gombe Mr. Gregory Tukumbor y ace umurnin hana jam’iyyar APC shiga zaben da za a sake din ya fito ne daga Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Yola. Hasali ma, in ji shi, lokaci ya wuce APC ba ta gabatar da takardun shirin shiga zaben ba. To amma dan takarar da kotun ta soke zabensa, Alhaji Umaru Barambu y ace shi fa zai shiga zaben saboda abin da kotun ta ce kawai shi ne bai bi ka’ida ba lokacin da ya fice daga jam’iyyar PDP. Barambu y ace zai yi takarar ce karkashin APC.

To amma kakakin jam’iyyar APC a jahar Gombe, Mr. Bili Garba y ace abin da su ka sani shi ne kotu ta hana Barambu ne tsayawa takara amma ba APC ba. Saboda haka jam’iyyar APC za ta shiga takarar.

Ga wakilinmu Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG