Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliyawa 11 Sun Bayyana Gaban Kotu A Amurka


An kama wadannan Somaliyawa a bayan da suka kai farmaki kan jiragen ruwan yakin Amurka biyu cikin teku a gabar gabashin Afirka bisa zaton cewa jiragen 'yan kasuwa ne

Wasu Somaliyawa su 11 da ake kyautata zaton ‘yan fashi cikin teku ne sun bayyana a gaban wata kotun tarayya a nan Amurka bisa tuhumar kai hari a kan wasu jiragen yaki guda biyu na Amurka a teku a gabar gabashin Afirka.

An kama biyar daga cikin mutanen ranar 31 ga watan Maris a bayan musayar wuta da jirgin ruwan yakin Amurka mai suna USS Nicholas, su kuma sauran shidan an damke su a bayan da suka yi harbi kan jirgin ruwan yakin Amurka mai suna USS Ashland a farkon wannan watan.

Dukkan Somaliyawan 11 sun bayyana gaban kotun jiya jumma’a a garin Norfolk dake Jihar Virginia, mai makwabtaka da nan birnin Washington domin su saurari irin tuhume-tuhumen da ake yi musu. An bayar da umurnin a ci gaba da tsare su har zuwa ranar laraba, ranar da za a yi zaman sauraron ko ya kamata a bayar da belinsu.

Takardar tuhume-tuhumen da aka bayyana ta jiya jumma’a ta nuna cewa ana tuhumarsu da fashi cikin teku, kai hari domin yin fashi a cikin jirgin ruwa, kai farmaki da mugun makami da kuma yin amfani da bindiga wajen aikata laifi.

Yin fashi cikin teku ya zamo matsala babba a teku a daura da gabar gabashin Afirka, inda a cikin ‘yan kwanakin nan gungu gungun ‘yan fashi suka kara azamar kai hare-hare duk da kasancewar akwai jiragen ruwan yaki na kasashe da dama su na sintiri a yankin.

XS
SM
MD
LG