Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia: Yadda Bam Ya Kashe Mutum Hudu a Ranar Sallah


Akalla farar hula hudu ne suka mutu yayin da wasu 15 suka jikkata bayan da wani bam ya fashe yayin bikin Eid al Fitr a wajen garin da ake kira Baidoa da ke Somalia, a cewar shaidu.

Biyu daga cikin wadanda suka mutu yara ne, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Fashewar ta faru ne da tsakiyar ranar Lahadi, yayin da mutane ke yin wani taron rawar gargajiya a wani fili da ke kusa da sansanin ‘yan gudun hijirar da ke arewacin garin.

Somalia ta yi bikin Eid al Fitr ne a ranar Asabar amma an ci gaba da bikin wanda za a kwashe kwana uku ana yi bisa al'ada a kasashen Musulinci.

Wani jami’in tsaro da ya ce kada a ambaci sunansa, ya ce an gudanar da bikin ne a filin a ranar Asabar ba tare da wata matsala ba.

Amma a cewarsa an dasa bam din ne kafin a ci gaba da bukukuwana washe garin ranar Lahadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG