Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliya: An Yi Zanga Zanga Kan Tsaurin Dokar Killacewa


Zanga zangar da aka yi ranar Jumma'a a Somaliya
Zanga zangar da aka yi ranar Jumma'a a Somaliya

Daruruwan masu zanga zanga sun bazu kan tituna jiya Asabar a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, don nuna bacin ransu kan abin da su yi zargin cewa kuntatawa ce ta jami’an tsaron gwamnati.

Zanga zangar ta biyo bayan harbin wasu fararen hula biyu har lahira da wani dan sanda ya yi, a kokarin tilasta jama’a su kiyaye dokar takaita yawo saboda cutar coronavirus, da daren jiya Jumma’a.

Masu zanga zangar, wadanda ke dauke da kwalayen sakonni, sun yi ta daga murya su na kalaman Allah wadai da gwamnati, su na ta cinna ma tayoyi da kuma hotunan Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed wuta.

“Kar ku kashe mu a yayin da mu ke fama da matsanatan matsaloli masu nasaba da cutar coronavirus,” a cewar daya daga cikin sakonnin.

Da asubahin jiya Asabar, masu zanga zangar su ka yi dandazo a katafaren dandalin tsakiyar birnin su na kiran da gwamnati ta yi adalci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG