Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliya Za Ta Gayyaci Kamfanonin Hako Mai


Ma'aikatan bangaren mai Somaliya
Ma'aikatan bangaren mai Somaliya

Yayin da kasar Somaliya ke gab da shiga sahun kasashe masu arzikin man fetur, gwamnatin kasar ta ce ta na shirin gayyatar kamfanonin hako man fetur su shigo a hada hannu a ci arziki

Gwamnatin Somaliya ta ce za ta bayar da lasisin hako mai ga kamfanonin kasashen waje, duk kuwa da kiraye-kirayen ‘yan adawa cewa a jira har sai an bullo da ka’idoji da kuma dokokin tafi da bangaren mai na kasar.

Binciken karkashin kasa da wasu kamfanonin Burtaniya biyu su ka yi, wato da Soma Oil & Gas da kuma Spectrum Geo, ya nuna cewa kasar Somaliya na da arzikin mai a ta bakin gabarta da tekun Indiya, a tsakanin biranen Garad da Kismayo. Adadin mai da ke wajejen na iya kai wa ganga biliyan 100.

Gwamnatin dai ta ce za ta saurari masu takarar samun lasisi a ranar 7 ga watan Nuwamba, kuma nan take za a sanar da wadanda su ka yi nasara. Ta ce za a rattaba hannu kan yarjajjeniyar raba ribar a ranar 9 ga watan Disamba, ta yadda kuma za a fara aiwatar da yarjajjeniyar ranar 1 ga watan Janairun 2020.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG