Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma Ya Kai Karar Wata Jarida Yana Zargin Ta Bata Masa Suna.


Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma

Cikin karar,Mr. Zuma yana neman diyyar dala dubu 700,000.00, daga jaridar Sunday Times,shekara daya kamin ya zama shugaban kasa.

Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma ya shigar da kara kan zane da wata jarida ta yi a 2008 da yace ya bata masa suna da muzanta shi.

Mr. Zuma yana neman jaridar Sunday Times, ta biya shi dala dubu dari bakwai,kan zane da jaridar ta wallafa kamin ya zama shugaban kasa da yace ya zubar masa da mutunci. A zanen anga Mr. Zuma yana kwance mazarginsa yayinda magoya bayansa suka danne mutum-mutumin matan nan ta alamar shari’a.

Mai zanen,Jonathan Shapiro, wanda yake da inkiyar “Zapiro” a shafin zanensa yace zanensa kamace kurum.

An wanke Mr. Zuma kan zargin fyade a 2006,a 2008 kuma wani alkali ya yi watsi da duk zargin cin hanci da rashawa da ake masa. Karar tana neman tarar dala 570,000.00,san nan wasu dala dubu 140,000.00,kuma saboda batawa shugaban kasan suna

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG