Hukumomi a Andalus ko Spaniya, sun ce za su takaita zirga-zirgar jama’ar kasar mai yawan mutumn miliyan 46, a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus da ke bazuwa a nahiyar turai.
A jiya Asabar jami’ai a Madrid, babban birnin kasar ta Andalus, suka ce za su kwaikwaiyi irin matakin da hukumomin Italiya suka dauka na rufe daukacin kasar har na tsawon mako biyu.
Firai Ministan Spaniya, Pedro Sanches ya ce wannan mataki wanda zai fara aiki nan take, zai haramtawa mutane fita daga gidajensu, sai dai idan za su je sayen abinci ko magani ko kuma mutum zai je taimakawa wadanda ke bukatar a kai musu dauki.
Jami’ai a kasar ta Spaniya sun ce an samu sama da mutum 5,700 da suka kamu da cutar ta COVID-19, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 136.
Hakan dai na faruwa ne a yayin da jama’a a Turkiyya suke ta rububin tanadin kayayyakin masarufi da magunguna, tun bayan da hukumomin kasar suka bayyana samun mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar.
"Da misalin karfe takwas da rabi na safe na bude shago, amma ya zuwa karfe sha-dayan rana komai ya kare, kuma farashin kayayykin sun yi tashin goron zabi. Na damu matuka da yadda al’amura ke tafiya.” In ji Hatice Guvenkaya, ma’aikaciya a wani shagon sayar da magani a kasar ta Turkiyya.