Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka na Gab da Amincewa START


wasu samfurin manyan makaman da aka girke
wasu samfurin manyan makaman da aka girke

Majalisar Dattawan Amurka ta kawar da wata babbar matsala game da batun cimma sabuwar yarjajjeniyar rage makamai da Rasha

Majalisar Dattawan Amurka ta kawar da wata babbar matsala game da batun cimma sabuwar yarjajjeniyar rage makamai da Rasha, ta kuma amince da kada kuri’a ta karshe game da yarjajjeniyar, mai suna Sabuwar Yarjajjeniyar Rage Manyan Makamai.

Jiya Talata, ‘Yan Majalisar Dattawan kada kuri’a 67 na masu rinjaye da kuma 28 na marasa rinjeya wanda hakan ya bayar da damar daina cigaba da muhawara kan batun saboda a kai ga batun amincewa ta karshe da yarjajjeniyar, wadda ta na ma iya yiwuwa yau Laraba. Kusan ‘Yan Republican 12 suna goyon bayan yarjajjeniyar, wanda ke nuna cewa ana iya samin akalla kashi biyu cikin uku mai rinjaye da ake bukata don tabbatar da dokar a Majalisar mai mutane 100.

Gwamnatin Amurka ta yanzu na daukar wannan yarjajjeniyar a matsayin ginshikin kyautata dangantaka tsakanin tsoffin abokan gaba na zamanin yaki cacar baka. Amincewa da wannan zai tabbatar da nasara ga Shugaban Amurka Barack Obama game da manyan manufofinsa na kasashen waje kafen Majalisar ta tafi hutun wannan shekarar.

Tun da farko dai Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates ya ce amincewa da yarjajjeniyar cikin lokaci za ta inganta tsaron Amurka.

Wasu ‘yan Republican sun ce Majalisar Dattawan ba ta da cikakken lokacin yin muhawara kan yarjajjeniyar, kuma basu yadda da kada kuri’ar amincewa ba a daidai lokacin da wannan Majalisar ke kawowa ga karshe. Sanata Lindsey Graham daga Carolina ta Kudu ya ce yarjajjeniyar za ta shafi dadadden burin Amurka dinnan na girke makaman kariya daga makamai masu linzami.

XS
SM
MD
LG