Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Stephen Hawking Ya Rasu


Stephen Hawking
Stephen Hawking

An yi wani babban rashi a fagen ilimin kimiyya, mumamman ma a bangaren nazarin duniyoyi, sanadiyyar rasuwar shahararren masanin kimiyya Stephen Hawking.

Shahararren masanin kimiyyar duniyoyin nan na Burtaniya Stephen Hawking, wanda ya yi ta nazarin maudu’o’i iri-iri da su ka shafi duniyoyi - kama daga yadda su ka samu, zuwa yadda su kan shude su zama wani bakin rami mai zurfi, wanda ake kira black hole, ya mutu yau dinnan Laraba ya na mai shekaru 76 da haihuwa.

Wani mai magana da yawun iyalinsa ya ce Hawking ya mutu salun-alun a gidansa da ke birnin Cambridge, inda ya shafe shekaru gommai ya na aiki a matsayin Sheihin Malamin Lissafi na Jami’ar Cambridge.

“Ya kasance wani mashahurin masanin kimiyya kuma wani irin mutum da ba a sama gani ba; sannan ayyukansa za su cigaba da yin tasiri zuwa shekaru masu yawa,” a cewar ‘ya’yan Hawking, Lucy da Robert da kuma Tim a wani bayanin da su ka yi.

Tun ya na dan shekaru 21 da haihuwa ya kamu da wata cutar nakasa, wadda sannu a hankali ta sa ala tilas ake sa shi cikin wata kujera ta musamman kuma ya daina magana sai ta amfani da na’ura mai fassara manufar mutum.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG