WASHINGTON, DC —
Liverpool da Manchester United duk sun huta kafin wannan wasan kece raini na gobe lahadi da zasu gwabza.
A wasan karshe da ta buga kafin karon battar da za a yi yau lahadi, Liverpool ta je har gidan Southampton ta lallasa ta da ci 3 da 1. Wasa na hudu ke nan da ‘yan Liverpool suka lashe a jere, kuma ‘yan gabanta sun jefa kwallaye har 15 a wadannan wasannin guda hudu.
Sai dai kuma, hutun da aka samu na wasannin kasa da kasa da kuma tsarin wasannin lig-lig sun sanya makonni biyu ke nan ‘yan Liverpool su na motsa jiki kawai ba tare da sun buga wani wasa ba. Masu fashin baki suka ce watakila makonnin biyu sun ba manajan Liverpool, Brendan Rodgers, sukunin yin karin gishiri a irin tamaula mai burgewa da ‘yan kungiyarsa ke takawa a wannan kakar kwallon kafa ta 2014. Yanzu dai, wata biyu da rabi ke nan babu wanda ya doke Liverpool a fili.
Ita kuma a nata bangaren, Manchester United , ta lallasa West Bromwich Albion da ci 3 da babu a bayan hutun wasannin kasa da kasa da aka yi. Akwai namijin aiki a gaban ‘yan Red Devils domin a bayan ziyarar da ‘yan Liverpool suke kai musu gobe lahadi, kungiyar Olympiakos ma zata ziyarci Old Trafford domin zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai, inda ita Olympiakos take gaba da kwallaye biyu a karawar farko da suka yi.
Amma babban abinda ke gaban manajan Manchester United, david Moyes, shi ne samun maki 3 a gwabzawar yau da Liverpool domin kungiyarsa ta kasance tana da sukunin iya shiga cikin masu zuwa gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai a shekara mai zuwa.
A yanzu dai Manchester United tana lamba ta 6 a teburin lig na Firimiya. Idan ta samu nasara a yau, tana iya zamowa maki 8 kawai ya raba tsakaninta da Liverpool.
Hanya mafi sauki da Manchester United zata iya kaiwa ga matsayi na 4 domin shiga gasar ta zakarun kulob kulob a badi, ita ce ta fara lashe wasanninta baki daya, sannan kuma kungiyoyin Liverpool da Arsenal su fara shan kashi a wasanninsu.
Liverpool da Manchester United duk ba su cikin manyan masu tsaron baya, amma sun bambanta a ‘yan wasan gabansu, inda Luis Suarez na Liverpool ya rika narka kwallo cikin raga a farkon kakar kwallon bana. Koda yake ya dan yi sanyi yanzu, irin ‘yan baya na Manchester United ba zasu iya hana shi jefa kwallo ba, watakila.
Daniel Sturridge kuwa har yanzu da zafinsa. Idan ka fitar da kwallon da ya jefa ma Ingila, Sturridge ya jefa kwallaye guda 9 a wasanni 10 na Liverpool da suka shige. Duk da cewa bai shiga dukkan wasannin kungiyar ba, Sturridge yana da kwallaye 18 bana, kuma shi ne na biyu a duk kasar Ingila a bana wajen yawan kwallaye a wasan nin lig-lig na firimiya.
Amma dai, Hausawa su kan ce ba a san ma ci tuwo ba, sai idan miya ta kare.