Accessibility links

Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma yarjajjeniya kan kudin man fetur


Sudan / South Sudan Talks
Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma yarjajjeniyar kawo karshen takaddama kan kudin mai, kuma za su tattauna kan lokacin da za a dawo da bin ta Sudan wajen jigilar man Sudan ta Kudu zuwa kasashen waje, wani mai shiga tsakani daga Kungiyar Tarayyar Afirka ne ya bayyana hakan a yau dinnan Asabar.

Sudan ta Kudu wacce ba ta da wata kafar teku, ta daina sarrafa mai a cikin watan Janairu bayan da ita da Sudan su ka kasa cimma maslaha kan kudin da ya kamata ta biya don ta cigaba fitar da manta ta bututan Sudan.

“Wannan jarjajjeniya ce da ta shafi dukkannin al’amuran. Muhimman batutuwan dai su ne kudin jigila, da sarrafawa da kuma dako,” a ta bakin tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, wanda shi ne kungiyar Tarayyar Afirka ta tura shi don shiga tsakani wato Thabo Mbeki a bayaninsa ga ‘yan jarida.

Bai bayar da cikakken bayani ba, kuma babu wani martani nan take daga Sudan da Sudan ta Kudu, wadanda su yi ta tattaunawa kan yadda za su kawo karshen rashin jituwar, a Hidikwatar MDD da ke birnin Addis Ababa.

XS
SM
MD
LG