Wasu daga cikin jam’iyyun siyasa na bangaren ‘yan adawa a Sudan ta Kudu, wadanda suka rattaba hannu a wata yarjejeniya da aka kulla a Khartoum, sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda a samu wanzuwar zaman lafiya, duk da cewa ba su amince da wasu sharruda da ke kunshe a matsayar da aka cimma ba.
Kungiyar raya kasashen gabashin Afirka ta IGAD, ta fitar da wata sanarwa a jiya Talata, inda ta ce masu shiga tsakanin da suka hada da shugaban Sudan, Omar Al Bashir, za su ci gaba da shimfida hanyoyin tattaunawa, har sai an rattaba hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa.
Facebook Forum