‘Yan siyasa da masu sharhi kan demokaradiyya da sauran ‘yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da kin sanya hannu da shugaba Muhammadu Buhari yayi akan daftarin gyaran dokar zabe da majalisar kasar tayi.
A hirarsa da Muryar Amurka, Alhaji Sule Lamido guda cikin dattawan Jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ya bayyana mamaki kan yadda shugaban kasar yayi watsi da gyaran fuskar da majalisar dokokin ta yiwa dokar zaben.
A ganinsa Shugaba Buhari ya yi hakan ne saboda gujewa kaddara wanda son kai ke haifarwa. Gudun kaddara ya kan sa abunda ake gujewa ya tabbata, inji Sule Lamido.
Rashin sa hannun shugaban kasa akan dokar ya ba Alhaji Sule Lamido mamaki. Ya ce "ana cewa Buhari ikon Allah soboda haka tunda ikon Allah ne sai ya sa hannu a daftarin ya bar Allah ya yi aikinsa."
A cewarsa idan Shugaba Buhari na ganin kin sa hannu shi zai sa ya ci zabe nan gaba yana gudun kaddara ne. Wato tamkar shugaban ya bar Allah ke nan ya koma ga tsarin mutum.
Akan dalilin da shugaban kasa ya bayar na kin sa hannu domin hanyoyin da
'yan majalisa suka bi sun sabawa kundun tsarin mulkin kasar, Alhaji Sule Lamido ya ambaci wadanda suka karya doka a karkashin shugaban amma bai san akwai doka ba sai yanzu da za'a yi gyaran dokar zabe, a cewarsa?
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da ci gaba da firar
Facebook Forum