Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Yiwu Kashe Kansu 'Yan Matan Nan Biyu Su Ka yi- In Ji 'Yan sanda


Tala Farea da Rotana Farea

A wani al'amari mai daure kai, an tsinci gawarwakin 'yan mata biyu 'yan'uwan juna, kuma 'yan asalin kasar Saudiyya a wani kogi da ke birnin New York, a yayin da iyayensu su ka bukaci su koma gida Saudiyya.

Hukumar 'yan sandan birnin New York ta ce 'yan matan nan 'yan'uwan juna, 'yan asalin kasar Saudiyya, wadanda aka tsinci gawarwakinsu a gabar kogin Hudson da ke Manhattan, da alamar kashe kansu su ka yi.

Dermot Shea, Shugaban sashin bincike na rundunar 'yan sandan New York, ya ce rahotanni sun nuna cewa Tala Farea, yar shekaru 16 da haihuwa da kuma 'yar'uwarta Rotana Farea, yar shekaru 23 da haihuwa, sun gwammace kashe kansu da komawa gida Saudiyya.

Shea ya ce da alamar 'yan matan sun shiga cikin kogin da ransu kuma da kansu.

Da alamar 'yan matan, wadanda su ka kasance a Amurka na tsawon shekaru uku, an yi ta gallaza ma su kuma sun bukaci mafaka a nan Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG