Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Suna Jin Tsoro Ne – inji Tambuwal


Kakaki Aminu Waziri Tambuwal ya zanta da Muryar Amurka. (File Photo)
Kakaki Aminu Waziri Tambuwal ya zanta da Muryar Amurka. (File Photo)

Idan za’a iya tunawa a ‘yan kwanakin nan, wasu muhimman ‘yan Najeriya sunyi kira akan a jinkirta gudanar da zaben shekarata 2015, saboda kalubale da matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta, tare da kafa gwamnatin rikon kwarya.

To sai dai Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayyar Aminu Waziri Tambuwal, a lokacin da yake kaddamar da yakin neman zabensa a matsayin gwamnan Jihar Sokoto, yayi kakkausar suka akan lamarin, wanda yace ya sabawa kundun tsarin mulkin Najeriya.

Tambuwal yace “ina so in shaida muku cewa, babu wani abu makamancin gwamnatin rikon gadi a tanade-tanaden kundun tsarin mulki. Zabin da kawai ake da shi shine shirya zabe sahihi bisa adalci.”

“Ai wannan suna jin tsoro ne, domin kuwa ina da yakinin cewa, jam’iyyar APC ce zata kafa gwamnati mai zuwa idan har aka gudanar da zabe.”

Taron kaddamar da dan takarar a Sokoto, wanda ya samu hallartar shugaban jam’iyyar na kasa Chief John Oyegun, da Bola Ahmed Tinubu da ma gwamonin Kwara da Edo, ya mayar da hankali ne akan halin da Najeriya take ciki na tabarbarewar al-amura, abunda gwamnan Jihar Adams Oshiomole yace ya kai halin “La Haula”.

“A yanzu, zabe da za’a yi, babu maganar kai daga ina kake. Abunda yake kasa shine, wane ne zaiyi aiki da gaskiya, a gani cewa idan talaka ya kwanta bacci ya tashi, baya jin tsoro”, a cewar Oshiomole.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG