WASHINGTON, DC —
Najeriya ta gayyato Joseph Yobo a karon farko cikin shekara guda da watanni, yayin da aka ki gayyatar sanannu kamar su Sunday Mba, Brown Ideye, John Ogu, Nnamdi Oduamadi da Chigozie Agbim.
A yau ‘yan Super Eagles na Najeriya suke karawa da Mexico a Atlanta, inda ake sa ran yin abin tarihi, za a ga yawan mutanen da ba a taba gani ba don wasan kwallon kafa a filin wasa na Georgia Dome dake Atlanta. Ya zuw aJumma’a, an sayar da tikiti dubu 54.

Watanni 10 da suka shige, Najeriya da Mexico sun gwabza a Houston a nan Amurka inda suka yi kunnen doki da ci 2-2.
Wannan wasa yana da matukar muhimmanci ga kwach na kasar Mexico, Miguel Herrera, domin wannan ce dama kwaya daya tak da yake da ita ta ganin yadda ‘yan wasansa na cikin gida da na waje zasu taka kafin ya yanek shawarar wadanda zasu buga wa kasar a ainihin gasar cin kofin duniya.