Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria Zata Yi Gwanjon Gidajen Wadanda Suka Gudu Saboda Yakin Basasa.


Shugaba Assad na Syria.

Hukumomin kasar sun bada wa'adi zuwa 10 ga watan Mayu mai zuwa su gabatarwa hukumomi takardun shaidar mallakar gidajen, ko kuma su rasa su.

A Syria, gwamnatin kasar ta shirya zata kwace gidajen miliyoyin 'yan kasar wadanda suka tsere daga muhallan su, idan basu dawo suka nuna takardun shaidar mallakar wadannan gidajen ba.

Karkashin dokar da aka bullo da ita cikin watan nan, 'yan kasar milyan 6 wadanda suka gudu domin kaucewa yakin da ake yi, da kuma wasu milyan bakwai (7) wadanda aka raba da muhallan su zuwa wasu sassan kasar, an basu wa'adin zuwa 10 ga watan Mayu mai zuwa, suyi rijistar gidajen su, ko kuma su rasa su.

Sauran fulotan, gwamnati zata yi gwanjon su karkashin dokar da aka kira doka lamba 10.

Ana jin msu zuba jari karkashin mabiya akida ko masahabar Alwite tsiraru a Syrian akidar da shugaba Bashar al-Assad yake bi, sune zasu tafka dan karen riba karkashin wannan shiri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG