Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Hanyar Raya Ilimi Ne Za Mu Yaki Talauci A Tsakanin Al’umma – Sheikh Yahaya Jingir


Taron Shekara Na Gidauniyar Ilimi Ta JIBWIS A Birnin Abuja
Taron Shekara Na Gidauniyar Ilimi Ta JIBWIS A Birnin Abuja

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala na Najeriya Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ta hanyar raya ilimi ne kungoiyoyin addini za su ba da gudunmawa wajen yaki da talauci da miyagun dabi’u.

Shehun malamin na magana ne a taron shekara na gidauniyar raya ilimi da makarantu da kungiyar ta gabatar a Abuja.

Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce tun kafa kungiyar ta dauki matakan kafa makarantu da jan hankalin jama’a wajen muhimmancin neman ilimi don kawar da jahilci da kuma bunkasa zamantakewar alheri tsakanin jama’a.

Malamin ya ce al’umma ba za ta shiga halin ni ‘ya su ba matukar ta na bin dokokin Allah da kuma hakan ke yin nasara ta hanyar ilimin sanin Allah.

Taron Shekara Na Gidauniyar Ilimi Ta JIBWIS A Birnin Abuja
Taron Shekara Na Gidauniyar Ilimi Ta JIBWIS A Birnin Abuja

Da ya ke karfafa muhimmancin ayyukan kungiyar na raya ilimi, Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid ya ce kungiyar ta na da makarantu a ko ina a fadin tarayyar Najeriya inda jama’a kawai na bukatar shiga ne don samun karatu.

Mai masaukin baki a taron shugaban majalisar malamai na Abuja Sheikh Ibrahim Duguri, ya ce aikin cibiyar ilimi ta kungiyar da ke Abuja na ci gaba da gudana har kusan an kammala aikin ta.

Taron Shekara Na Gidauniyar Ilimi Ta JIBWIS A Birnin Abuja
Taron Shekara Na Gidauniyar Ilimi Ta JIBWIS A Birnin Abuja

Babban bako a taron tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya ce ba abun da jama’a za su bayar ya zama ya yi kadan ta hanyar gudunmawa ko zuba jari ga raya ilimi.

A yanzu haka JIBWIS ta tura malamai birane da kauyuka har ma da wasu kasashe na Afurka ta yamma don gudanar da tafsirin watan ramadan.

Domin Karin bayani ga rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG