Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta’addanci: Kwararru Sun Ce A Sa Ido Kan Masu Dawowa Daga Libiya


Wasu 'yan Najeriya kenan da aka maido daga kasar Libiya na jira a masu rajister

Ganin yadda ake ta maido da wasu 'yan Najeriya daga kasar Libiya, wadda ta'addanci ya daidaita, wasu kwararru kan tsaro sun ce ya kamata hukumomi su sa ido sosai kan wadanda ake maido da su Najeriya saboda kar a shigo da wadanda su ka rungumi akidar 'yan ta'addan ISIS.

A yayin da ake cigaba da jigilar ‘yan Naijeriya daga kasar Libiya zuwa gida Najeriya, wasu kwararru sun ce ya kamata hukumomi su kula sosai kar wajen kwaso ‘yan Najeriya a kwaso har da wasu miyagu. Su ka ce ya kamata a rika tantancewa sabots kar a debo har da wadanda su ka samu horo daga kungiyar ISIS.

Kwamrad Abdullahi Yelwa, Shugaban Sashin Nazarin Miyagun Dabi’u da kuma yadda za a tsai da yaduwarsu na Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Tatari Ali da ke Bauchi y ace ya kamata a nazarci yanayin kasar ta Libiya don a san yadda ta ke a halin yanzu da kuma irin matakin da ya kamata a dauka. Ya ce saboda yawan ‘yan Najeriya, wasu mutane kan yi karyar cewa su ‘yan Najeriya ne alhalin kuwa babu abin da ya hada su da Najeriya. Ya ce wasu daga cikin irin wadannan masu shigowa Najeriya ba bisa ka’ida ba, su ke haddasa matsaloli.

Wani masanin harkokin tsaron kuma mai suna Malam Hamza Umar Usman ya ce irin wannan batu na da hadarin gaske. Don haka y ace idan aka kawo irin wadannan mutanen kamata ya yi a killace su a yi nazarin hankalinsu a kuma tabbatar da asalinsu da kuma inda su ka sa gaba kafin a sake da su.

Ga wakilinmu Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG