Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabar Sigari Na Hallaka ’Yan Najeriya Sama Da Dubu 29 A Kowacce Shekara


Wani mai shan tabar sigari
Wani mai shan tabar sigari

Wani rahoto cibiyar bincike kan tattalin arzikin nahiyar Afirka ya bayyana da cewa akalla ’yan Najeriya 29,472 ne suke mutuwa a kowacce shekara sakamakon shan tabar sigari.

Ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan a yayin jawabi a bikin ranar yaki da shan sigari ta duniya a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda ya ce rahoton da cibiyar bincike kan tattalin arzikin nahiyar Afirka ta wallafa na shekarar 2021 ne ya tabbatar da hakan.

Taken bikin ranar yaki da shan sigari ta duniya na bana shi ne “Yadda za a kaucewa shan tabar sigari” wanda ya zo a daidai lokacin da aka fi bukatarsa, musamman duba da yadda duniya ta dukufa wajen yaki da annobar COVID-19 da ta yiwa kasashe katutu.

Kwararan hujjoji sun nuna yadda masu ta’ammali da taba sigari suka fi barazanar kamuwa da cututtuka masu yaduwa, ciki har da cutar Korona birus, saboda haka, taimakawa jama’a wajen wayar da kan su kan ilollin shan tabar sigari zai taimaka wajen yaki da shan ta, a cewar minsitan lafiya.

Osagie Ehanire
Osagie Ehanire

Haka kuma, Dakta Osagie Ehanire ya bayyana cewa, shan sigari kan haifar da kamuwa da cututtuka da suka hada da hawan jini, shanyewar barin jiki, ciwon sukari, cutar sankara da kuma wasu cututtukan.

A yayin jawabi a taron bukin ranar yaki da shan sigari ta duniya, daraka mai kula da nahiyar Afirka ta hukumar lafiya ta duniya wato WHO, dakta Matshidiso Moeti, ta ce hukumar ta zabi Najeriya tare da ragowar kasashe 22 domin shirin tallafawa mutane su daina shan sigarin tun suna matasa.

Matshidiso Moeti ta yi kira ga minista Osagie Ehanire da ya kafa cibiyoyin tuntuba a duk fadin kasar wadanda za'a aike musu da kwararru domin ganawa da jama’a kai tsaye tare da magance musu matsalolinsu kan daina shan tabar sigarin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG