Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tafiyar Shugaba Buhari Zuwa Birtaniya


Shugaba Mohammadu Buhari

A lokacin da yake ban kwana kafin tafiyar sa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yace ya riga ya shaidawa ‘yan kasar cewa zai yi tafiya tsawon kwanaki goma zuwa Birtaniya don duba ciwon kunnen da yake fama da shi.

Shugaban dai wanda tun farko ya kwanta a Asibitin fadarsa ta Aso Rock, ya nuna alamun gajiya tun a jawabin da yayi na ranar dimokaradiyya. Shugaban yace ya shaidawa Majalisa wannan tafiya da zai yi don haka ya nuna barin madafun iko ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

A wata tambaya da akayi masa na cewa me zai cewa ‘yan Najeriya musamman ma wadanda suka afka zulumi don wannan tafiya? Buhari dai cewa yayi “Akwai mutumin da baya rashin lafiya”.

Wannan dai itace tafiya ta farko a hukumance da shugaban yayi don duba lafiyarsa tun hawa mulki a bara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG