Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Kan Hukuncin Kotu: An Hallaka Mutane Hudu A Jahar Taraba


Sabuwar Gwamnar Jahar Taraba, Sanata A'isha Jummai Alhassan.

Bangarorin APC da PDP na cigaba da cece-kuce kan hukuncin kuton daukaka kara, wadda ta soke zaben Gwamna Darius Ishaku a matsayin gwamnan jahar Taraba.

Mutane hudu sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama su ka ji munanan raunuka sakamakon taho-mu-gama da matasa magoya bayan jam’iyar APC da PDP suka yi a garin Wukari na jihar Taraba. Wannan kuwa ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara, wadda ta bai wa ‘yar APC Sanata Aisha Jummai Alhassan nasara a karar zaben gwamnan jahar.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Taraba Alkali Shaba wanda ya tabbatar da barkewar sabon rikicin, wanda ya abku lokacin da Matasan APC suka fita kan tiunan Wukari suna shagulgulan murnan hukunci da kotun sauraron korafe-korafen zabe ta ba da umurnin hukumar zabe ta mika wa Sanata A’ishatu Jummai Alhassan kujerar gwamna jihar Taraba.

A halin da ake ciki kuma, an shiga cece-ku ce tsakanin Mr. Darius Ishaku na APC da Kotun ta soke zabarsa jiya da kuma bangaren APC, Mr Darius ya jaddada cewa ya daukaka kara saboda bai amince da hukuncin kotun ba. Mai bai wa gwamnan shawara a fuskar siyasa Alhaji Abubakar Bawa y ace sam ba a masu adalci ba, saboda an bar batun zaben gwamna an koma batun zaben fidda dan takara.

Ga wakilanmu Sanusi Adamu da Ibrahim Abdul’aziz da cikakkun rahotannin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

XS
SM
MD
LG