Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Kan Makomar Kungiyar Biyafara


Shugaban kungiyar tawayen Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu

Batun ko shin ya cancanta a kira kungiyar Biyafara kungiyar ta'addanci ko wani suna dabam na cigaba da daukar salon siyasa a Najeriya, bayan da aka shiga zargin shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da neman siyasantar da batun.

Duk da lafawar da rikicin biyafara ya yi, ana cigaba da tafka muhawara kan ayyana kungiyar Biyafara a matsayin kungiyar ta’addanci da hukumar sojin Najeriya ta yi kwanan baya, duk da ya ke wasu rahotanni na nuna cewa hukumar sojin ta Najeriya ta janye wannan mataki.

Wannan takaddamar kuwa ta yi tsanani ne saboda yadda bangaren gwamnatin Najeriya ya nuna alamar ya na mai ra’ayin cewa ‘yan Biyafaran sun cancanci sunan ‘yan ta’adda kamar yadda sojojin Najeriya su k ace; a yayin da kuma Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ke cewa bai daje a kira ‘yan Biyafara ‘yan ta’adda haka kwatsam ba tare da an tantance tasirin yin hakan ba.

Ganin yadda matsayin Shugaban Majalisar Dattawan ya janyo sukar gaske daga wasu ‘yan Najeriya masu ra’ayin cewa Mr. Nnamdi Kanu da sauran ‘yan kungiyar ‘yan tawayen IPOB ta Biyafara ‘yan ta’adda ne, shugaban Kwamitin Labaru na Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Aliyu Sahabi, ya ce ba a fahimci manufar Sarakin ba ne. To amma ya bai wa ‘yan Najeriya wadanda su ka fusata da matsayin Sarakin hakuri.

Ga Sale Shehu Ashaka da cikakken labaran:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG