Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kawo yanzu ‘yan takara goma sha daya ne suka fito a inuwar jamiyar PDP domin tsayawa takaran kujeran gwamnan jihar Adamawa.

Kawo yanzu ‘yan takara goma sha daya ne suka fito a inuwar jamiyar PDP domin tsayawa takaran kujeran gwamnan jihar Adamawa.

Yayin da ya rage kwanaki hamsin da hudu a gudanar da zaben chike gurbin gwamnan jihar Adamawa, wata sabuwa ta kunno kai na neman wanda jamiyar zata tsayarda.

A wani bangare kuma wasu manyan kusoshin jamiyar ta PDP ke zawarcin tsohon hukumar EFCC Malam, Nuhu Ribadu, da yazo ya tsayamata takara batun da yanzu ya jawo cece kuce a jamiyar.

To anya ba rashin da takara bane yasa kungiyar ke zawarcin wasu daga waje, Barrister, Shehu, sakataren jamiyar PDP a jihar da Adamawa, yace jamiyar PDP bata fito tace tana neman wani daga waje ya tsayamata takara ba.

Shi kuwa Alhaji Ibrahim Tukur, mai son Ribadu, ya tsaya takara a inuwa jamiyar PDP cewa yayi” lallai mun gani a jaridu da maganganun mutane a kasidu ana cewa Nuhu in yazo ba za’a karbe shi a PDP ba yace leman PDP zai dauki kowa.”

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG