Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Zaben Fidda Gwani a Jam'iyar APC


Muhammadu Buhari, da wasu jigajigan APC.

An bayyana cewa talakawa, Janar Muhammadu Buhari suke bukata ya tsaya takarar neman shugabancin Najeriya.

An bayana cewa talakawan Najeriya, Janar, Muhammadu Buhari suke bukata ya tsaya takara neman shugabancin Najeriya, wani na hannun damarsa Abdulmajeed Dan Bilki ne ya bayana haka ga wakilin muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari.

Saida masu fashin baki akan siyasa sun fara tsokaci akan yanda zaben fida gwani na jamiyar APC ka iya kasancewa, a cikin jamiyar Bashir Hayatu wani mai sharhi akan siyasa, yace janar Buhari, shine alherin APC, kuma shine matsalarta.

Dalili inji shi, shine idan babu Buhari kuri’un da jamiyar ta APC ke zaton samu ba zata samu ba, kuma yace matsalar kuma shine, yawancin mutane masu fada aji, ba zasu goyi bayansa ba, amma yana da goyon baya a kasa.

Ya kara da cewa kashi 70 cikin 100 na ‘yan APC, a arewacin Najeriya, dake jamiyar, APC suna yi ne don janar Buhari.

Batun fitowar takaran Gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara raba kawunan ‘yan jamiyar APC, masamman ‘yayan Kwakwasiya, a jihar Kano.

Shi kuwa Rabiu Abdullahi garin Danga, wani dan kwankwasiya cewa yayi Janar, MUhammadu Buhari, yana da kima, a idon duniya, saboda ya amincewa Rabiu Musa Kwankwaso, takara shi kuwa yazo yayi jagora.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG