Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talakawan Karkara Na Tababan Farfadowar Tattalin Arzikin Najeriya


Masu kananan sana'o'i

Yayinda gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce alkalumma sun nuna tattalin arzikin kasar ya fita daga masasshar da y afada ciki su ko talakawan karkara cewa suke har yanzu basu gani a kasa ba

Hukumar kula da alamuran kidigdiga ta Najeriya ce ta fito da wasu alkalumma dake bayyana cewa kasar ta fita daga komadar tattalin arziki da kasar ta fada ciki a shekarun baya.

To amma masu kananan sana'o'i da wadanda suke tafiyar da harkokin kasuwancinsu a yankunan karkara sun ce har yanzu basu gani a kasa ba dangane da ikirarin na gwamnatin Najeriya cewa kasar ta fita daga komadewar tattalin arziki.

Wani Ibrahim Suleiman daga karamar hukumar Tofa yace sana'rsa dinki amma har yanzu bai ga wani sauyi ba a harkokinsa.Shi ko Hamisu Muhammad cewa ya yi farfadowar tattalin arzikin kasa suna jinsa ne kawai. Amma ta bangaren sana'arsa yadda yake samu da, yanzu ba ya samu. A bangaren dinkin hannu shi bai ga farfaowarsa ba.

Wani mai wanke huluna da yin guga ya ce babu abun da ya sake. Watakila nan gaba za'a samu canji amma yanzu kam ana nan kamar jiya.

Amma wani magidanci a cewarsa an samu cin nasara sanadiyar damina mai kyau da aka samu amma bai kamata gwamnati tace ta samu nasara ba. Injishi an dade ba'a samu albarkatun gona irin na bana ba.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG