Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban sun fasa zaman tattaunawa da Afghanistan


Mullah Omar shugaban kungiyar Taliban

Amurka na kira ga sababbin shugabannin Taliban da aka bayyana a jiya Juma’a cewa sun zabi masu maye gurbin Mullah Omar da su bada kai.

Wajen halartar taron da Amurka ta kira da sahihin sulhun kawo zaman lafiya tsakanin Taliban da gwamnatin Kabul. Wani babban jami’in Amurka mai aiki akan tsarin kawo zaman lafiya a Afghanistan Jakada Daniel Feldman ne ya bayyana haka.

Taliban dai sun soke haduwar da aka tsara yi a jiya Juma’a jim kadan kafi fara taron na tsakaninsu da gwamnatin Afghanistan. Sai yanzu suka sanar da cewa, Mullah Akhtar Mansoor ne makwafin Mullah Omar da ya kafa kungiyar Taliban, sun kuma boye mutuwarsa fiye da shekaru biyu.

Jakadan Amurkan yace, in aka ce ga yadda abin zai kasance to anyi gaggawa, amma Amurka na fatan ganin zaman sasantawar ya yiwu don a zauna lafiya. Sannan ya bayyana 'yan taliban da tsantsar kungiyar asirin da ta boye mutuwar shugabanta shekaru biyu.

XS
SM
MD
LG