Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kungiyar Agaji Ta Red Cross


A wani mataki na bazata, kungiyar Taliban ta canza ra'ayinta na dakatar da kungiyar agaji ta Red Cross, ta na mai alkawarin bayar da kungiyar agajin kariya don gudanar da harkokinta na jinkai a Afghanistan.

A jiya Lahadi kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta janye dakatarwar da ta yi wa kungiyar bada agaji ta Red Cross, kuma ta maido da tabbacin kariyar da a baya ta bai wa mai’aikatan kungiyar ta ICRC wadanda ke aikin ba da agaji Afghanistan.

“Masarautar Islama ta maido da alkawarin tabbatar da tsaro ga 'yan kungiyar bada agaji da ICRC a Afghanistan, kuma ta umarci dukan shahidai da su kauce wa hanyar da kungiyar ICRC ta ke gudanar da ayyukanta, kuma su kula da tsaron ma’aikatan kungiyar da kuma kayakinsu,” a cewar wata takardar bayani ta kungiyar ta Taliban ta.

Maimagana da yawun kungiyar agaji ta ICRC ya ce ranar ta yi daidai da ranar da kungiyar ta koma da ayyukanta a cikin fadin kasar ta Afghanistan.

Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG