Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taraba: An Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Hannu A Kisan Hakimin Sarkin Kudu


Rundunar Yan Sandan Najeriya
Rundunar Yan Sandan Najeriya

Rundunar 'yan Sandan jihar Taraba ta yi nasarar kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan hakimin Sarkin Kudu da ke karamar hukumar Ibbi a jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Usman Abdullahi Jada, ya ce wadanda ake tuhumar suna ba jami’an da ke binciken lamarin hadin kai, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Idiris Adamu shi ne kanin marigayi wanda har ila yau ya lmarin, ya ce mutane hudu sun afkawa gidan dauke da bindigogin a hannayensu.

Shigarsu gidan ke da wuya suka tambayi dakin Hakimin a daidai lokacin da ya ji hayaniya ya fito a cewarsa.

Kuma nan take suka sare shi da adda, lamarin da ya sa shi komawa dakin da ya fito suka kuma afka masa, tare da harbinsa da bindiga wanda nan take Allah ya dauki rayuwarsa.

Wasu daga cikin mazauna garin birnin Kudu sun koka kan matsalar rashin tsaro a yankinsu, tare da neman dauki daga gwamnatocin jiha da tarayya.

Domin karin bayani saurari rahotan Lado Salisu Garba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG