Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taraba: Jam’iyyun Adawa Sun Zargi Gwamnati Jiha Da Cin Zarafin Ma’aikata


Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba Haruna Manu a Taron Masu Ruwa Da Tsaki

Hadakar jam'iyun adawa a jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya sun zargi gwamnatin jam’iyyar PDP a jihar da cin zarafin ma'aikata da kuma wasu sarakuna da ke dasawa da wasu jam'iyyun siyasa a, zargin da gwamnatin jihar ke musantawa

Yayin da ya rage yan kwanaki kafin babban zabe a Najeriya, yanzu haka wata sabuwa ta kunno, inda a jihar Taraba jam'iyun hamayya ke zargin gwamnatin PDP da nuna barazana ga ma'aikata da kuma sarakunan jihar da ke dasawa da yan hamayya.

A wajen taron manema labarai a Jalingo fadar jihar, jam'iyun adawa sunce yanzu haka sun bankado wani shiri da suka ce gwamnatin jihar ke yi ta bayan fage kan ma'aikata da sarakuna game da zaben dake tafe.

Shima da yake nasa jawabin, daya daga cikin shugabanin kungiyoyin kwadago a Najeriya, wanda ke zama darakatan kamfen na daya daga cikin yan takarar gwamna a jihar, Kwamared Bobboi Bala Kaigama, ya nuna bacin ransa game da abubuwan dake faruwa yanzu, inda ya zargi gwamnatin jihar da shakulatin bangaro, ya ce lokaci yayi na kawo sauyi.

To sai dai kuma gwamnatin PDP a jihar ta musanta wadannan zarge zargen da yan jam'iyun adawa ke yi yanzu.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Facebook Forum

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG