Tarayyar Turai (EU) ta ce ba ta san ko za a tsame ta daga cikin jerin kasashen da Shugaban Amurka Donald Trump zai sa haraji kan dalma da karafansu ba.
Yau Jumma’a a birnin Brussels Kwamishiniyar Harkokin Cinakayyar Tarayyar Turai Cecilia Malmstrom ta ce, “Mu na fatan za mu samu tabbacin cewa an tsame Tarayyar Turai daga wannan harajin.”
Trump ya rattaba hannu jiya Alhamis kan shelar sa haraji na kashi 25% kan kafaran da aka shigo da su, da kuma kashi 10% kan dalmar da aka shigo da ita, kuma harajin zai fara aiki ne sati biyu masu zuwa.
An tsame kasashen Canada da Mexico daga wannan harajin zuwa wani lokaci a yayin da ake cigaba da tattaunawa kan tsarin cinakayya mai walwala na kasashen Yankin Arewacin Amurka (NAFTA a takaice) tsakaninsu da Amurka.
Malmstrom ta ce Tarayyar Turai ba ta shirin shiga rigima da Amurka to amma a shirye ta ke ta mai da martani da haraji kan kayakin Amurka, wadanda ta ce za su hada da kayan kara dandanon abinci da kuma ruwan lemo.
Facebook Forum