Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ta Ce Bata Fifita Shugaba Buhari Ba a Zaben 2015


Shugaba Muhammad Buhari

Tsohon jagoran sa ido na tarayyar turai a zaben Najeriya na shekarar 2015, Santiago Fisher, ya musanta zargin cewa kungiyar ta fifita takarar Muhammad Buhari bisa sauran ‘yan takarar amma ya yabawa tsohon shugaban kasar Jonathan wanda bai bata lokaci ba ya amince ya sha kaye

Santiago Fisher, tsohon jagoran tawagar tarayyar turai da ta zo sa ido a zaben Najeriya na shekarar 2015, ya musanta zargin fifita Shugaba Muhammadu Buhari. Amma ya yabawa tsohon shugaba Goodluck Jonathan da amincewa da sakamakon zaben ba tare da wata hamayya ba. Santiago Fisher ya yi furucin ne a ziyarar da ya kai Abuja, babban birnin Najeriya.

Wani malamin jami’a, Farfesa Jibo Ibrahim ya nanata wa mutane su dinga yin tambaya kan abubuwan da basu gane ba gameda ‘yan siyasa. Ya kira jama’a da su daina dinke bakunansu idan wadanda suka zaba basa yin abinda suka zabesu su yi.

Shi ma ministan matasa na Najeriya, Solomon Dalung, ya ce talakawa ne suka jagoranci zaben shekarar 2015. Ya ce a zaben shekarar 2019 babu batun APC, halin mutum ne zai sa a zabeshi. Ya ce wadanda aka zabesu sanadiyar guguwar Buhari yanzu kashinsu ya bushe.

Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG