Accessibility links

Tarayyar Turai Ta Kakabawa Iran Takukumin Hana Sayen Mai Daga Kasar

  • Aliyu Imam

Ministan harkokin wajen Faransa Alin Juppe yake tattaunawa da takwarorinsa a taron EU.

Tarayyar turai ta tsaida shawarar aza takunkumin hana sayen mai daga kasar Iran.

Tarayyar turai ta tsaida shawarar aza takunkumin hana sayen mai daga kasar Iran.

Litinin din nan ne kungiyar mai wakilai 27 ta bayyana daukan wan nan mataki a birnin Brussels a kokarin dakatar da shirin Iran na habaka makaman Nukiliya.

Ministocin harkokin waje na kasashe dake cikin kungiyar wadanda ahalin yanzu suke taro a birnin Brussel din, zasu zayyana abinda wan nan kuduri zai kunsa.

Wadansu rahotanni suna cewa za a aza aza takunkumin ne daki daki cikin watanni masu zuwa.

XS
SM
MD
LG