Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ta Taimakawa Najeriya da Makudan Kudi Domin Kiwon Lafiya Matakin Farko


Tarayyar Turai ta taimakawa kiwon lafiya a Najeriya da dallar euro miliyan 70

Babban daraktan kiwon lafiya matakin farko na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasa Dr. Faisal Sha'aibu ya ba taron tabbacin yin anfani da taimakon dalar ero miliyan saba'in yadda ya dace

Kungiyar Tarayyar Turai da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO da hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya ko UNICEF suka hada taimakon domin kiwon lafiya na matakin farko a Najeriya.

An zabi jihohi biyar da zasu ci gajiyar taimakon, biyu daga arewa maso gabas Adamawa da Bauchi. A arewa maso yamma an zabi Kebbi da Sokoto sai kuma jihar Anambra daga kudu maso gabas.

Tarayyar Turai ta taimakawa kiwon lafiya a Najeriya da dallar euro miliyan 70
Tarayyar Turai ta taimakawa kiwon lafiya a Najeriya da dallar euro miliyan 70

Adadin kudin da za'a yi anfani dasu nan da zuwa shekaru uku nera miliyan dubu arba'in ne.

Rage mutuwar mata a lokacin haihuwa da samar ma jarirai abinci mai gina jiki na daga ayyukan da za'a yi da kudaden.

Adamu Ibrahim Gamawa shugaban hukumar kiwon lafiya matakin farko na jihar Bauchi yace an fi maida hankali akan yara kanana masu kasa da shekaru biyar da kuma mata.

Ita ma kwamishanar kiwon lafiya ta jihar Adamawa Fatima Abubakar tace samar wa al'umma cibiyar lafiya da bada magani kyauta daga tallafin babban abu ne na ajiyar zuciya.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG