A cikin bayani da yayi dangane da kasidar da ya gabatar a wajen taron, Pastor Yohana Boro, ana iya cimma hadin kai da zaman lafiya a Najeriya, muddin shugabanni da talakawa sun kudurin anniyar ganin haka.
Yohana yace, a dubi tarihi lokacinda ma kusan za'a ce babu kiristoci, maguzawa ne, kuma sun zauna lafiya da musulmi da sauran al'uma.
Ya bayyana cewa ki jama'a tareda shugabanni suke yi, domin idan suna so za'a sami hadin kai.
Yace kamar jama'a sun rungumi wata akida ce, da juyawa Allah baya.
Anasa bangaren, Dr. Isa Adamu, na jami'ar IBB dake Lapai, yace matsalar Najeriya cikin shekaru 30 da suka wuce shine rashin shugabanci. Baya ga haka sai matsalar cin hanci da rashawa, wadda malamin yace shine jigo cikin matsaloli dake hana ruwa gudu a Najeriya.
Ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ya dukufa wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da cikakken bayani
Facebook Forum